Connect with us

Labarai

Yajin Aikin ASUU-KASU Zagon Ƙasa ne – Kwamishina

Published

on

Kwamishinan illimi na jahar Kaduna, Farfesa Muhammad Sani Bello ya bayana yajin aikin Kungiyar malaman jami’a reshen jihar Kaduna ASUU-KASU a matsayin zagon ƙasa ga harkar cigaban jami’ar.

Farfesa Bello, ya bayana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ma mane ma labarai a ranar alhamis, kwana biyu da fara yajin aikin a Kaduna.

Sanarwa ta bayana cewa,” Tun daga shekarar 2009 zuwa 2024, reshen Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) ya shude tsawon shekaru 15 ba tare da murya ba. Sai dai a cikin ‘yancin da ta samu a yanzu, kungiyar ta rungumi yunkurin kawo tsaiko ga ci gaban jami’ar, ta hanyar shiga yajin aiki gaba daya, wanda ya fara ranar talata da ta gabata.

Takaddamar kungiyar da gwamnatin jihar Kaduna na da nasaba da rashin biyan albashin watanni biyar daga Mayu zuwa Satumba 2022 da kuma alawus-alawus na aiki daga 2015 zuwa 2020, da wasu bukatu.

Ba tare da kokwanto ba, wadannan bukatu sun shude tun kafin zuwan wannan gwamnati, amma gwamna Uba Sani, a cikin tausayi da jin kan sa, ya dauki matakai domin magance su tare da sauran bukatun jami’o’in da jihar ke da su baki daya.

Duk da haka, maimakon a bari a kammala aiwatar da matakan warware matsalar, ASUU ta dauki matakin nuna karfin iko, wanda ba wai kawai zai dagula kalandar karatu ta KASU ba, har ma da kawo cikas ga ci gaban da aka samu zuwa yanzu.

A gaskiya, mai girma gwamna ya amince da wasu daga cikin bukatunsu kuma ya yi alkawarin ganawa da shugabannin ASUU bayan dawowarsa daga tafiya, amma duk da haka, kungiyar ta dage kan yajin aikin.

Babu shakka, akwai wani shiri da wasu ke kullawa domin kawo cikas ga irin nasarorin da gwamnatin gwamna Uba Sani ta samu a fannin ilimi a cikin watanni 20 da suka gabata. Wasu ‘yan baranda da ke fakewa da sunan kungiya na kokarin jefa makomar ‘ya’yanmu cikin garari.

Na tsawon shekaru ASUU ta nemi ganawa da gwamnatin da ta shude, amma bata samu nasara ba. Sai dai a ranar 18 ga Disamba, 2024, gwamna Uba Sani ya gana da shugabannin jami’o’in da na kungiyoyin malamai na dukkan manyan makarantu mallakin jiha tsawon sa’o’i uku.

A lokacin taron, an tattauna batutuwa kuma an cimma matsaya. Amma ASUU na kokarin jefa cikas ga yarjejeniyar da aka kulla. Babban batun da aka fi mayar da hankali a kai shine batun albashi da jin dadin ma’aikata.

Mai girma gwamna ya amince da biyan kudaden da aka tara tun zamanin gwamnatin da ta gabata, amma a bisa sharadin cewa za a biya su sannu a hankali, duba da yanayin tattalin arzikin jihar.

Haka nan, malamai sun bukaci a rika ware kudade na gudanar da makarantu a kullum. Mai girma gwamna ya bada tabbacin cewa za a fitar da sabon tsarin rarraba kudaden, wanda zai kai ga fitar da jami’o’i daga tsarin TSA (Treasury Single Account).

Babu shakka, gwamna Uba Sani na da burin kawo zaman lafiya a bangaren ilimi da kuma daukaka harkokin jami’o’i zuwa matakin ci gaba. Amma ASUU reshen KASU, bisa ga wani shiri da ke kunshe, na kokarin haddasa rudani da rufe jami’ar gaba daya.

Mai girma gwamna Uba Sani ba wai kawai yana kishin jin dadin ma’aikatan KASU da sauran manyan makarantu na jihar ba ne, har ma yana kokarin mayar da su cibiyoyin nagarta. Amma saboda ASUU ta kasa fahimtar hakikanin lamarin, gwamnatin jihar Kaduna za ta aiwatar da tsarin “ba aiki, ba albashi” a duk tsawon lokacin da yajin aikin zai dauka.”

Copyright © 2024 kaduna Reports.