Wani makiyayi da akalla shanu 12 sun mutu sakamakon tsawa a Matuak Giwa, cikin Gundumar Bondon, Masarautar Moro’a, da ke Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yamma a ranar Lahadi, yayin da mamacin ke tare da shanunsa yana neman mafaka daga ruwan sama. Sai tsawa ta fado mu su, suka mutu nan take.
A cewar Hakimin Matuak Giwa, Simon Ayuba, lamarin ya girgiza al’ummar yankin, kasancewar hakan ba karamin iftila’i ba ne.
“Makiyayin tare da shanu 12 sun mutu nan take. Wannan lamari ne mai matukar ban tausayi kuma ya jefa al’umma cikin tashin hankali,” in ji shi.
Shugaban makiyaya na Gundumar Bondon, Mallam Tanko Isiyaka (Ardo), ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa marigayin asalin dan Jihar Bauchi ne.
“Mun yi matukar bakin ciki da wannan rashi. Muna rokon Allah Ya jikansa. Ya kamata mu ci gaba da addu’a da kuma tallafa wa iyalansa,” in ji Isiyaka.
Mutane da dama a yankin sun bayyana alhininsu kan wannan lamari, inda wasu ke ganin ya kamata a kara wayar da kai kan yadda ake kare kai daga hadurran tsawa musamman a lokacin damina.