A ranar 10 ga Afrilu, 2025, wata guguwa mai tsanani ta afkawa Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Agunu Dutse, a Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Guguwar ta yi mummunar barna ga ajujuwa da dama da al’ummar yankin suka gina da haɗin gwiwar juna.
kamar yadda jaridar yanar gizo ta Inside Kaduna, ta walafa a shafin ta na Facebook.
Sakamakon rushewar ajujuwan, makarantar ta shiga cikin mawuyacin hali, inda ɗalibai suka rasa wuraren da suka dace da su ci gaba da karatu. Ajujuwan da suka lalace na daga cikin ginin da ke wakiltar jajircewar al’umma wajen ganin an samu ingantaccen ilimi duk da ƙarancin tallafin gwamnati. Lalacewarsu ta rage wa ɗalibai kwarin gwiwa tare da jefa iyaye cikin damuwa.
Duk da haka, al’umma sun sake ɗaukar mataki. Shugabanni, iyaye da wasu masu kishin yankin sun fara haɗa kudi da kayan aiki domin sake gina ajujuwan da suka rushe. Sai dai ƙalubale na kuɗi da kayayyaki na hana ci gaba aikin da gaggawa.
Yanzu haka, al’umma na kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta gaggauta kawo ɗauki. Suna roƙon a tallafa wajen sake gina ajujuwan da kuma ɗaukar matakan gyara matsalolin da makarantar ke fuskanta tun tuni.