Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Yadda Amfani da Fasahohin Zamani Zai Taimaka Wajen Kare Makarantu a Fadin Najeriya – Dr. Kanyip

Published

on

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gida na Jihar Kaduna, Dr. James Kanyip, ya bukaci a rungumi sabbin fasahohi domin kare makarantun Najeriya daga hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Yayin gabatar da jawabi a taron kasa karo na biyu na Tsangayar Ilimi ta Jami’ar Veritas, Abuja — wanda ya samu halartar masana da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi — Dr. Kanyip ya bayyana cewa tsaron makarantu ya zama wajibi idan ana son kare makomar ilimi da ci gaban kasa.

Ya ce fasahohin zamani kamar kyamarorin CCTV da ke amfani da AI, jiragen sama marasa matuki (drones), na’urorin tantance mutum ta hanyar zane yatsu, da tsarin gaggawa na bada agaji na iya sauya tsarin tsaro gaba ɗaya.

Dr. Kanyip ya tunasar da harin da aka kai Kuriga, Jihar Kaduna, inda aka sace dalibai 287 da malaminsu. Ya ce tsoron irin wadannan hare-hare na daga cikin manyan dalilan da yasa yara da dama ba sa halartar makaranta, musamman a yankin Arewa.

Qididdiga ta nuna cewa yara sama da miliyan 13.5 ba sa zuwa makaranta a Najeriya — mafi yawansu daga Arewacin Najeriya.

Kwamishinan ya bayyana matakan da Gwamnatin Kaduna ke dauka, ciki har da shirin “Safe Schools Initiative” wanda ke kunshe da katangar kariya, na’urorin gano motsi, da tsarin gargadi, da kuma Smart City Project wanda ke amfani da kyamarori da AI wajen gano barazana da hanzarta daukar mataki.

Ya ce duk da fa’idar fasaha wajen hanawa da dakile hare-hare, akwai kalubale kamar rashin isassun kudade, matsalolin cibiyar sadarwa, da karancin kwararru.

Dr. Kanyip ya bukaci hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, da kuma horar da jami’an tsaro don cimma nasara.

Ya kammala da kira ga al’umma da su dauki tsaron makarantun yara a matsayin hakkinsu na dan Adam da nauyin da ke wuyan kowa.
Aqalla sama da yara miliyan 13.5 ne qididiga ya nuna ba sa zuwa makaranta a Najeriya, wanda mafi yawa daga cikin yaran sun fito ne daga yankin Arewacin Nijeria.

Ya bayyana matakan da Jihar Kaduna ke dauka, ciki har da shirn (Safe Schools Initiative), wacce ke kunshe da katangar kariya, na’urorin bincike da tsarin gargadi kafin hare-hare, da kuma Smart City Project wanda ke amfani da kyamara da AI wajen gano barazana da hanzarta daukar mataki.

Dr. Kanyip ya ce duk da irin fa’idar fasaha wajen hana hare-hare da hanzarta daukar mataki, akwai kalubale da suka hada da rashin kudade, gurbatacciyar cibiyar sadarwa da rashin kwararrun ma’aikata.

Ya bukaci hadin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu tare da horar da jami’an tsaro domin cimma nasara.

Ya kammala da kira ga daukacin al’umma da su dauki tsaron makarantun yara a matsayin hakkinsu na ɗan adam da kuma alhakin kasa.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.