Bayan matsalolin da aka fuskanta sakamakon lalata kayan wutar lantarki a Karamar Hukumar Kagarko, an fara aikin dawo da hasken wutar lantarki karkashin jagorancin Shugaban Karamar Hukuma, Hon. Muhuyideen A. Umar, da hadin gwiwar Gwamna Malam Uba Sani.
A yau ne Hon. Muhuyideen tare da tawagarsa suka karɓi kayan aikin da aka saya domin aikin sake haɗa wutar lantarki a Kagarko LG. Wannan aiki yana cikin tsarin gwamnatin APC ta jihar Kaduna na “Light Up Kaduna”, wanda Gwamna Uba Sani ke jagoranta domin kawo ci gaba da jin daɗin al’umma.
Lamarin wutar lantarki ya daɗe yana janyo ƙorafe-ƙorafe a tsakanin jama’a a Kagarko, kuma yanzu gwamnati ta nuna ƙudurin gyarawa tare da kawo mafita mai ɗorewa.
Yayin karɓar kayan aikin, Hon. Muhuyideen ya nuna godiya ga Gwamna Uba Sani bisa wannan gagarumin mataki. Ya kuma ja hankalin al’ummar Kagarko da su ci gaba da goyon bayan gwamnati tare da kula da kayan aikin wutar, ta hanyar gaggauta bayar da rahoto idan an ga wani yana aikata laifi ko lalata kayan aiki.
“Wannan aiki na haɗa wutar lantarki zai amfanar da kowa da kowa. Muna buƙatar hadin kan jama’a domin a kammala aikin lafiya kuma a kare shi daga masu laifi,” in ji Hon. Muhuyideen.
A cikin kasafin kuɗin karamar hukumar na shekarar 2025, an ware naira miliyan 50 domin dawo da wutar lantarki a fadin Kagarko. Daga ciki:
Naira miliyan 15 za a yi amfani da su wajen gyaran kayayyakin wuta.
Naira miliyan 35 kuma domin siyan sabbin transfoma da girka su a fadin karamar hukumar.