Hanyar Rigachikun – Tami – Birnin Yero da ke Karamar Hukumar Igabi na cigaba da samun ci gaba, godiya ga kokarin da gwamnatin Gwamna Uba Sani ke yi.
Wannan aiki na daga cikin kudirin gwamnatin jiha na inganta ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki.
Ginin wannan hanya mai tsawon kilomita 25 ana sa ran zai hade fiye da al’ummomi 50, ya saukaka zirga-zirgar jama’a da kayayyaki (musamman kayayakin amfanin gona), kuma zai yi tasiri mai kyau ga tattalin arzikin yankin.