Labarai

Uba Sani Ya Samu Lamabar Yabo Kan Gwamna Da Yafi Kokarin Kan Kula Da Muhali Na Shekarar 2025

Published

on

Fadar shugaban kasa Nijeria ta karama gwamna jahar Kaduna Sen. Uba Sani da lamban yabo na gwamna da yafi kokari akan kula da muhali.

Bikin ya gudana a dakin liyafa na fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar talata inda aka karrama gwamnan Jihar Kaduna da lambar yabo a matsayin gwamna mafi kokari a fannin kula da muhalli (Environmental Health Stewardship Award).

Kwamishinan muhalli da albarkatun kasa, Hon. Abubakar Buba, shine ya wakilci mai girma gwamnan jihar Kaduna a wajen bikin bayar da lambar yabo ta ƙasa kan kyautata muhalli, wato National Environmental Health Excellence Award 2025.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, wanda ya wakilci shugaban kasa da babban kwamandan askarawan Najeriya, shi ne ya gabatar da lambar yabon.

Copyright © 2024 kaduna Reports.