Gwamna Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya karɓi baƙuncin Jakadan Amurka a Najeriya Mai Girma Mr. Richard M. Mills Jr, a gidan gwamnati dake Kaduna.
A safiyar yau talata ne, dai gwamna ya karɓi baƙuncin Jakadan Amurka a Najeriya, a zauren majalisar na gidan Sir Kashim Ibrahim, dake birnin Kaduna.
Uba Sani da jakadan sun tattauna batutuwan da suka shafi ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Amurka da Gwamnatin jihar Kaduna, musamman a fannonin bunƙasa ƙwarewa, da kuma zuba jari a muhimman sassa kamar Lafiya, Ma’adinai, Ilimi, da Noma.
A cikin jawabinsa, Jakadan ya yaba wa gwamnatin Uba Sani saboda shirin haɗin kai da kirkire-kirkiren da ta ke yi wajen samar da zaman lafiya, da farfaɗo da bangaren ilimi da kiwon lafiya. Ya ce tsarin lafiyar jihar abin koyi ne da ya kamata sauran jihohi su yi koyi da shi.
Har ila yau, ya jinjinawa gwamnati jihar Kaduna saboda jawo hankalin masu zuba jari zuwa Kaduna ta hanyar samar da ingantattun manufofi, bayar da kyawawan tallafi ga masu zuba jari, da kuma nuna ƙarfin hali wajen aiwatar da tsare-tsare. Ya bayyana cewa manyan kamfanonin Amurka sun nuna sha’awar zuba jari a jihar Kaduna.
A cikin bayani gwamnan, Uba Sani ya tabbatar wa Jakadan da tawagarsa cewa gwamnati jihar Kaduna zata ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Amurka, samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci da saka jari, da kuma ƙirƙirar sabbin tsare-tsare da shirye-shirye domin inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna.