A yau Asabar, Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta halarci bikin TUK HAM 2025 a matsayin bakuwa ta musamman.
A jawabinta, Dakta Hadiza ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta ci gaba da tallafawa al’adu domin karfafa zumunci da hadin kai tsakanin al’ummomin jihar.
Ta ce, “Bambancin da ke tsakaninmu ba zai raba mu ba, sai dai ya kara mana armashi, ya hura wutar kirkire-kirkire, ya kuma karfafa nufinmu na gina al’umma mai adalci da fahimta. Muna murnar bambance-bambancenmu, kuma a ciki muke samun karfin ci gaba tare.”
Mataimakiyar Gwamnan ta bayyana cewa bambancin al’adu shi ne karfin Jihar Kaduna. Ta ce hadin kai a cikin bambanci yana koya wa mutane juriya, mutunta juna da kuma ci gaba cikin hadin kai.
Ta kuma jaddada cewa yin amfani da al’adu ta hanya mai kyau zai taimaka wajen samar da zaman lafiya, cigaba da kuma karfafa dunkulewar al’umma a Kaduna da ma Najeriya baki daya.
A nasa jawabin, Shugaban kwamitin shirya TUK HAM, Ambasada Bulus Lolo (Sardaunan Ham), ya bayyana cewa bukin na da nufin godewa Allah kan girbin da aka samu da kuma neman albarka a sabuwar damina.
Ya roki gwamnatin jihar Kaduna da ta gyara titunan yankin, samar da ruwan sha mai tsafta, da kuma mayar da kananan masarautu 19 da aka rushe. Ya kuma bukaci majalisar tarayya da ta sauya sunan karamar hukumar Jaba zuwa Ham.
A nata jawabin maraba, Shugabar karamar hukumar Jaba, Larai Sylvia Ishaku, ta jaddada muhimmancin al’adu ga al’ummar Ham, inda ta ce: “Al’adu su ne muhallin asalinmu. Mu kiyaye su, mu yada su da alfahari.”
Bikin ya kunshi raye-rayen gargajiya, nune-nunen al’adu da jawabai daga manyan baki.