Siyasa
Shugaban kasa ya baiwa Sen. Suleiman Hunkuyi Mukami a Hukumar Majalisar Dokoki
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Dr. Saviour Enyiekere a matsayin Shugaban Hukumar Aikin Majalisar Dokoki ta Kasa (NASC) na tsawon shekaru biyar, tare da naddin membobin daga ko wace shiya.
An zabi Sen. Suleiman Othman Hunkuyi a matsayin memba na hukumar daga shiyar Arewa maso Yamma.
Kafin naɗinsa, Enyiekere, ƙwararre a fannin kula da muhalli, shi ne mataimakin shugaban ma’aikata na Shugaban Majalisar Dattawa.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya amince da naɗin mutane biyu daga kowanne yanki na ƙasar nan domin zama mambobin wannan hukuma.
Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a kan bayanai da tsare-tsare ya sanar da hakan a ranar alhamis a cikin wata sanarwa d ya fitar.
Sabbin mambobin su ne:
AREWA MASO YAMMA
(a) Suleiman Othman Hunkuyi
(b) Hon. Yusuf A. Yusuf Tabuka
AREWA MASO GABAS
(c) Aminu Ibrahim Malle
(d) Alhaji Lawan Maina Mahmud
AREWA TA TSAKIYA
(e) Mark Hanmation Tersoo
(f) Salihu Umar Agboola Balogun
KUDU MASO YAMMA
(g) Hon. Taiwo Olukemi Oluga
(h) Hon. Afeez Ipeza-Balogun
KUDU MASO GABAS
(i) Hon. Dr. Nnanna Uzor Kalu
(j) Festus Ifesinachi Odii
KUDU MASO KUDU
(k) Patrick A. Giwa
(l) Mrs. Mary Ekpenyong
Kamar yadda ya ke ga shugaban hukumar, sauran mambobin za su riƙe mukamansu na tsawon shekaru biyar, tare da yiwuwar sabunta wa.