An gudanar da tantancewar ɗaliban da suka nemi tallafin karatu na shugaban karamar hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad Jaga, jiya Lahadi a sakatariyar karamar hukumar dake Zariya.
Tantancewar ta shafi ɗaliban da suka cika sharudda kuma aka gayyace su domin tantacewa ta sakon waya.
Kamar yadda Abdullahi Abubakar, Jami’in Hulɗa da Jama’a, Kwamitin Shawara kan Ilimi, Karamar Hukumar Zariya ya sanar.
Tallafin na a tsara shi ne don ɗaliban da ba su iya biyan kuɗin rajista ba a manyan makarantu.
Yawancin ɗaliban da aka tantance sun fito daga Nuhu Bamalli Polytechnic da Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), tare da wasu daga makarantu daban-daban.
Kwamitin ya ce ya yi aiki tare da makarantu don tabbatar da sahihancin bayanan ɗaliban da kuma tantance waɗanda suka cancanta.
Ɗaliban da suka nemi taimako tun da fari amma suka ci bashi saboda jinkiri suma an sa su a cikin jerin.
Za a tuntuɓi waɗanda suka yi nasara a mako mai zuwa, sannan za a fara biyan kuɗi nan take.