A ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025, shugaban karamar hukumar Lere, Hon. Jafaru Ahmed, ya karɓi shugabannin Kungiyar Matasa Masu Rajin Cigaban Saminaka (SAYPA) a ofishinsa da ke Saminaka, hedkwatar karamar hukumar.
Ziyarar ta nuna ƙara wayewar matasa game da shugabanci nagari da ci gaban al’umma.
Shugabannin SAYPA sun yaba da ayyukan raya al’umma da ake gudanarwa a Lere, ciki har da tituna, kiwon lafiya, da inganta noma. Sun bayyana cewa ayyukan suna taimaka wa rayuwar jama’a kai tsaye.
Hon. Jafaru ya tabbatar da cewa gwamnatin karamar hukumar za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan da suka shafi matasa, ilimi, lafiya, da tsaro. Ya ce matasa suna da muhimmiyar rawa wajen cimma burin ci gaban al’umma.
Shugaban ya kuma gode wa Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, bisa goyon bayan da yake bai wa karamar hukumar Lere. Ya ce shugabancin gwamnan na taimakawa wajen sauya fasalin yankin.
A ƙarshe, Hon. Jafaru ya ƙarfafa matasa su ci gaba da haɗa kai don tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a Lere. Ya ce makomar yankin na hannun matasa, kuma lokaci ya yi da za su taka rawar gani.