Shugaban karamar hukumar Kachia Dr. Manzo Daniel Maigari, ya amince da naddin Hon. Yahaya Maigida a matsayin shugaban ma’aikata karamar hukumar tare da Zachariah Waje a matsayin mataimaki na musaman akan abun da ya shafi masu ruwa da tsaki da kuma tattaunawa da jama’a.
Bayanin naddin mukaman na kunshe ne a cikin wata takarda da tafito daga offishin shugaban karamar hukumar ta kachia dauke da sa hanun sa a ranar 23 ga watan mayun 2025.
Naddin na nuni da yadda gwamnatin karamar hukumar ke son tabatar da shugabanci nagari tare da tattaunawa da jama’a don samun cigaba da wakilci jama’a yadda ya kamata.
Haka zalika shugaban karamar hukumar ya taya sabin mataimakan nasa murna da musu fatan alheri a yayin gudanar da ayyukan su.