Kwamared Jerry Adams, Shugaban Hukumar Kudin Shiga Na Ciki Gida Ta Jihar Kaduna.
Shugaban Hukumar Kudin Shiga Na Ciki Gida Ta Jihar Kaduna (KADIRS), Kwamared Jerry Adams, ya fito fili ya karyata ikirarin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi kan kudaden shiga na jihar.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Kaduna, Adams ya musanta cewa gwamnatin da ta gabata tana tara naira biliyan 7 a kowane wata, yayin da ake cewa yanzu ana tara naira biliyan 2 kawai. Ya bayyana wannan ikirari a matsayin mara tushe, yana mai nuna cewa daga shekarar 2019 zuwa 2023, mafi girman kudin shiga da aka tara shine naira biliyan 59 a shekarar 2022—wanda ke nufin matsakaicin biliyan 4.9 a wata.
Ya kara da cewa, yawancin wadannan kudaden da aka tara a zamanin da sun samo asali ne daga kudaden haraji na baya da aka karbo (N22 biliyan) da kuma kudaden sayar da kadarorin gwamnati (N25 biliyan), wanda ya haura N45 biliyan gaba ɗaya. Idan aka cire wadannan kudaden da ba na yau da kullum ba ne, alkaluman kudaden shiga na gwamnatin da ta wuce sun fi karanci fiye da abin da ake yayatawa.
A bangaren ci gaba da aka samu a mulkin Gwamna Sanata Uba Sani, Adams ya bayyana cewa Kaduna ta samu kudin shiga na N62.48 biliyan a shekarar 2023, wanda ya karu zuwa N71 biliyan a shekarar 2024—wanda ke nufin matsakaicin tara na biliyan 5.2 da biliyan 6.0 a kowane wata, bi da bi.
A cikin watan Janairu da Fabrairu na 2025 kadai, Kaduna ta riga ta tara N14.16 biliyan—ba tare da dogaro da harajin baya ba.
Adams ya kuma karyata zargin cewa ana yawan cire naira miliyan 100 daga asusun kudaden shiga na jihar zuwa hannun wasu mutane. Ya tabbatar da cewa tsarin tara kudaden shiga na jihar yana tafiya ta hanyar zamani (automated), kuma ana shigar da dukkan kudaden ne kai tsaye cikin asusun gwamnati (TSA), wanda hakan ke hana duk wani cire kudi ta hanyar da ba bisa ka’ida ba.
Ya jinjina wa Gwamna Uba Sani saboda rungumar sauye-sauye irin su PAYKADUNA, wata sabuwar manhaja da aka ƙaddamar domin inganta gaskiya da inganci wajen tara kudaden shiga. A karon farko, Kaduna ta mallaki fasahar da take amfani da ita wajen karbar haraji, wanda hakan zai rage dogaro da kamfanoni masu zaman kansu tare da tabbatar da tsaro ga kudaden jihar.
Dangane da batun sauya shugabanci a KADIRS, Adams ya tabbatar da cewa tsohon Shugaban hukumar ya kammala cikakken wa’adinsa na shekaru hudu, sabanin jita-jitar cewa an tube shi ba bisa ka’ida ba.
“Jihar Kaduna ta ɗauki manyan matakai don ƙarfafa tushen kudaden shigarta. Ba ma dogara da kudaden da ake karɓo daga harajin baya kawai, amma muna mai da hankali kan ci gaba mai ɗorewa ta hanyar cibiyar bayanai guda daya da ke tattara dukkan kudaden shiga (centralized IGR database) da kuma tsarin dijital,” in ji Adams.
Ya tabbatar da cewa KADIRS za ta ci gaba da kasancewa mai gaskiya, kuma za ta rika wallafa bayanai na kudaden shiga da aka tabbatar a kai a kai.
“Tare da goyon bayan Gwamna Sanata Dokta Uba Sani, hukumomin gwamnati, da kuma al’ummar Kaduna—musamman masu biyan haraji—za mu ci gaba da jagorantar ci gaba da habaka tattalin arziki,” in ji shi.
Adams ya bukaci manema labarai da su rika bayar da rahotannin gaskiya, yana mai cewa hanya mafi dacewa ita ce a mai da hankali kan labarai da ke bunkasa Kaduna.