Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Siyasa

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sanata Suleiman Hunkuyi, a Matsayin Kwamishinan NASC

Published

on

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Saviour Enyiekere a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Majalisar Ƙasa (NASC), tare da wasu kwamishinoni 12 da ke wakiltar yankunan siyasa shida na Najeriya.

Taron rantsarwar ya gudana a zauren majalisar, Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, kafin fara taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC).

Daga cikin waɗanda aka rantsar akwai tsohon Sanatan Kaduna ta Arewa, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, wanda ya wakilci yankin a Majalisar Dattawa daga 2015 zuwa 2019.

Hunkuyi wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC kwanan nan, ya samu wannan mukami ne a matsayin wakilin yankin Arewa maso Yamma.

Shugaba Tinubu ya ja kunnen sabbin kwamishinonin NASC da su kasance masu gaskiya, ƙwarewa, da kishin ƙasa a yayin aiwatar da ayyukansu.

Ya ce hukumar na da muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan majalisa da samar da goyon baya ga ‘yan majalisa domin ingantaccen mulki.

A taron, an samu halartar Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume, da wasu manyan jami’an gwamnati.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.