Sen. Lawal Adamu, wanda ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, ya sake nuna jajircewarsa wajen taimakawa al’ummar mazabarsa, inda ya ware Naira Miliyan 500,000,000.00 domin saukaka wa jama’a a cikin wannan watan Ramadan.
Wannan tallafi na musamman zai taimaka wajen rage wahalhalun tattalin arziki da dama daga cikin al’ummar ke fuskanta, musamman a lokacin azumi.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Sen. Adamu ya bayyana cewa: “Watan Ramadan yana kara gabatowa, kuma domin saukaka wa al’ummar musulmi da sauran jama’a da za su yi azumi a wannan shekarar, na ware naira miliyan 500,000,000.00. Wannan taimako zai rage wahalhalu na tattalin arziki da mutane ke fuskanta a cikin wannan lokaci mai tsarki.”
Sen. Adamu ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwar abinci da su duba halin da mutane ke ciki, yana mai cewa: “Kodayake kasuwa na da muhimmanci, ya zama wajibi mu nuna jin kai da kuma sayar da abinci da sauran kayan bukatu a farashi mai sauki, domin taimaka wa wadanda ke cikin bukata.”
Ya kuma yi addu’a cewa: “Idan muka nuna rahama ga masu bukata a wannan watan na Ramadan, muna da yakinin cewa Allah zai nuna mana lada mai yawa.”
A ƙarshe, Sen. Adamu ya mika godiya ga duk wanda zai taimaka wajen saukaka wa al’umma, yana fatan wannan watan Ramadan zai kawo zaman lafiya, albarka, da karin nasara ga dukkanin al’umma. Ameen.