Labarai

Sarkin Ogbomoso Ya Kawo Ziyara Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna

Published

on

Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, a yau ta tarbi mai martaba sarkin Ogbomoso, Oba Ghandi Afolabi Olayele Orumogege III, yayin wata ziyarar ban girma a fadar Sir Kashim Ibrahim.

Sabon basaraken, wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2024, yana tare da tawagar ’yan asalin Ogbomoso da ke zaune a sassa daban-daban na jahar Kaduna. A lokacin ziyarar, Oba Afolabi ya bayyana burinsa na sauya Ogbomoso zuwa birni na zamani tare da jaddada aniyarsa na tuntubar al’ummar sa da ke zaune a wajen garinsu.

Sarkin ya jinjinawa salon shugabancin Gwamnatin jihar Kaduna da kuma kokarinta na inganta ci gaba a jihar. A martaninta, Mataimakiyar Gwamna Balarabe ta taya Oba murna bisa sabuwar sarautarsa tare da tabbatar masa da goyon bayan Gwamnatin jihar Kaduna.

Ta bayyana cewa jihar Kaduna na da cikakken kuduri na ba duk mazaunanta dama daidai, musamman ma tana yaba zaman lafiyar al’ummar Yarbawa da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa a ci gaban tattalin arzikin jihar.

Daga cikin manyan jami’an gwamnatin jihar da suka tarbi basaraken akwai Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Kwamishinoni, Sakatare Mai Zaman Kansa na Gwamna, Babban Sakatare na Yada Labarai na Gwamna, da kuma Mashawarta na Musamman.

Copyright © 2024 kaduna Reports.