Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Sanata Lawal Adamu Usman Ya Yi Allah-Wadai da Kisan ‘Yan Arewa a Edo, Ya Bukaci a Gaggauta Bincike

Published

on

Sanata Lawal Adamu Usman, Mai Wakiltar Kaduna Ta Tsakiya

Sanata Lawal Adamu Usman ya bayyana matuƙar takaici kan kisan gilla da aka yi wa wasu ‘yan Arewa a Jihar Edo, yana mai cewa wannan danyen aiki barazana ce ga zaman lafiya da haɗin kan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 28 ga Maris, 2024, Sanata Usman ya bayyana cewa waɗanda aka kashe ‘yan kasuwa ne masu neman halalinsu, amma aka hallaka su ba tare da wata hujja ba. Ya ce wannan ta’addanci ne da dole a dauki mataki akansa.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Edo, da hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike mai zurfi domin gano masu hannu a wannan aika-aika tare da tabbatar da cewa an hukunta su.

Haka kuma, Sanata Usman ya bukaci hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da shugabannin al’umma da su mayar da hankali kan tattaunawa da sulhu domin dakile rikice-rikicen kabilanci da ke barazana ga haɗin kai da ci gaban ƙasa.

Sanata Usman ya yi kira ga al’ummar Arewa da sauran ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su kwantar da hankalinsu, amma su dage wajen neman adalci ta hanyar doka. Ya ce bai kamata a bari wannan aika-aika ya haddasa rarrabuwar kawuna ko ramuwar gayya ba.

A cewarsa, “Ƙarfin Najeriya yana cikin haɗin kanmu. Dole ne mu ƙi tashin hankali kuma mu yi aiki tukuru don ganin an samu ƙasa mai adalci, zaman lafiya, da tsaro ga kowa.”

Sanata Usman ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, yana addu’a Allah Ya ba su ƙarfin jure wannan babban rashi. Ya kuma buƙaci ‘yan ƙasa da su ci gaba da haɗa kai wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya a ƙasar.

Copyright © 2024 kaduna Reports.