Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Rt. Hon. Zock ya Bada Tallafi Naira Miliyan 23 a Bikin Al’adar KORO 2025

Published

on

Rt. Hon. Gabriel Saleh Zock ya halarci bikin al’adar Koro da aka yi a Kubacha, cikin Karamar Hukumar Kagarko.

Ya ce zai bayar da Naira miliyan 20 don gina dakin taro na zamani ga al’ummar Koro.

Haka kuma, ya raba Naira miliyan 3 a matsayin kyaututtuka ga ƙungiyoyin kwallon ƙafa uku da suka yi fice a gasar da aka gudanar.

Zock ya bukaci Kungiyar Cigaban Al’ummar Koro da ta gabatar da cikakken shirin aikin, domin ofishinsa ya fitar da kudin yadda ya dace.

Zock shi ne dan majalisar wakilai mai wakiltar Kachia/Kagarko a Majalisar Tarayya, kuma shugaban kwamitin al’adu da yawon shakatawa.

Ya ce yana goyon bayan duk wani yunkuri da zai inganta al’adu da zaman lafiya a yankin.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.