Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana dalilin komawarsa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa zamanin mulkin Nasir El-Rufai ya zo karshe, kuma sabon Gwamnan Jihar Kaduna ya bude kofar sulhu da hadin kai.
A wata hira da ya yi a Channels Television, Shehu Sani ya ce:
“Na dawo APC ne saboda mulkin Mallam El-Rufai wanda ya lalata Kaduna ya kare, sannan sabon gwamna ya bukaci mu dawo mu yi sulhu da jam’iyya. Mun koma a matsayin rukunin da muka fita da shi tun farko.”
Sanatan ya kara da cewa ba za a sake daukar El-Rufai da muhimmanci ba a siyasar Najeriya. Ya bayyana hakan a matsayin abin dariya, ganin yadda tsohon gwamnan ke tunanin zai iya haifar da cikas ga gwamnatin tarayya.
“Yana da ban dariya yadda El-Rufai ke ganin zai iya kawo cikas ga gwamnatin tarayya, alhali a zaben da ya gabata APC ta fadi a Kaduna. An sha kasa a zaben shugaban kasa, an rasa kujerun Sanatoci uku, da tazarar kujeru tara daga cikin goma sha uku na majalisar wakilai.”
A lokacin mulkin El-Rufai, Shehu Sani ya fice daga APC zuwa jam’iyyar PDP, inda ya tsaya takarar gwamna a shekarar 2023.
Wannan dawowa tasa APC na nuna sabon shafi a siyasar Jihar Kaduna, musamman da sabuwar gwamnatin ke kokarin hada kan bangarorin siyasa domin zaman lafiya da ci gaba.