Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa burinsa na shugabanci shi ne samar da ci gaba mai daidaito ga kowane yanki na jihar, ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
A wata hira da aka yi da shi a shirin “Sunday Politics” na Channels Television, gwamnan ya ce rashin daidaito a ci gaba da siyasar addini da kabilanci sun raba kan al’umma, suna barin damar da ‘yan ta’adda ke amfani da ita wajen haddasa rikice-rikice.
“Lokacin da aka zabe ni a ranar 29 ga Mayu, na bayyana cewa ba zan yi la’akari da addini ko kabila ba wajen gudanar da mulki. Ina son ci gaban kowa da kowa,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta mayar da hankali wajen samar da ci gaba a yankunan da aka yi watsi da su a baya, musamman a Kudancin Kaduna, inda aka fara aiwatar da ayyukan raya kasa.
“Mun gano cewa akwai gibin ci gaba tsakanin birane da karkara. Don haka, mun fara mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa a yankunan da aka yi watsi da su,” in ji shi.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana aiki tare da shugabannin gargajiya da na addini domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a jihar.
A karshe, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da manufofin da za su tabbatar da ci gaba mai daidaito ga kowane yanki na jihar Kaduna.