Shugaban karamar hukumar Kagarko, Honourable Muhuyideen A. Umar, ya bukaci al’umma da su rungumi hadin kai da juriya don samun ci gaba mai dorewa.
Muhuyideen ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin da ya jagoranci bikin Koro Cultural Day Festival na shekarar 2025 a Kagarko.
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ce bakuwa ta musamman a bikin, wadda Kwamishinan Wasanni da Ci gaban Matasa, Prof. Benjamin Kumai Gugong, ya wakilta.
Taron ya samu halartar mataimakin kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, dan majalisar tarayya mai wakiltar Kachia/Kagarko, da kuma shugabannin kananan hukumomi na Soba, Kudan, Kaduna South, Jaba da Kachia. Dan majalisar jiha mai wakiltar Jaba da shugabannin addini da na gargajiya daga sassa daban-daban na jihar su ma sun halarta.
A jawabin sa, Muhuyideen ya ce, “Ba za mu samu ci gaba ba sai da zaman lafiya. Ba za mu samu zaman lafiya ba idan ba mu hade kai ba. Ba za mu hade kai ba idan ba mu jure wa juna ba.”
Ya gode wa Gwamna Uba Sani saboda cika alkawuran zabe da ya dauka ga al’ummar Kagarko.
Bikin Koro Cultural Day na daya daga cikin manyan bukukuwan al’ada da ke kara karfafa dankon zumunta a Kudancin Kaduna.