Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Mazauna Kapam sun yi zanga-zanga a NNPC Kaduna kan fitar sinadarin benzene

Published

on

Wasu mazauna unguwar Kapam da ke kusa da harabar Kamfanin tace mai na Kaduna (KRPC) sun gudanar da zanga-zanga a yau Litinin a kofar shiga NNPC da ke Kaduna.

Masu zanga-zangar sun ce sun fito ne domin nuna damuwarsu kan fitar sinadarin benzene da ya lalata gonaki da dukiyoyinsu tun watan Agustan bara.

Mafi yawan su sanye da bakaken kaya a matsayin alamar jimami, inda suka buƙaci gwamnatin tarayya da kamfanin su biya su diyya cikin gaggawa.

Prince Abello Samuel, ɗaya daga cikin masu zanga-zanga, ya shaida cewa KRPC ta yi alkawarin biyan diyya, amma har yanzu ba a cika ba.

“Kamfanin ya ce zai biya mu diyya saboda lalacewar gonakinmu, amma har yanzu muna jira babu wani abu da aka yi,” in ji shi.

Masu zanga-zangar sun toshe kofar shiga NNPC domin jawo hankalin hukumomi, suna mai cewa za su ci gaba da zaman dirshen har sai an saurare su.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.