Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Matsalar Ruwa Ta Kare a Maskawa: Hon. Munira Ta Kaddamar da Rijiyar Burtsatse Mai Hasken Rana

Published

on

Jama’ar garin Maskawa da ke cikin yankin Dan-Alhaji sun shiga cikin farin ciki da godiya bayan kammala aikin rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana (solar), wanda Hon. Munira Suleiman Tanimu ta kaddamar domin magance matsalar ruwa a yankin.

Hon. Munira, wacce ke wakiltar mazabar Lere East a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, kuma ita ce Shugabar Masu Rinjaye, ta kaddamar da wannan aiki mai muhimmanci wanda ke samar da tsaftataccen ruwan sha ga daukacin al’umma – yara, manya da tsofaffi.

Rijiyar burtsatse ta dauke nauyin matsalar da ta dade tana addabar al’ummar Maskawa. Mutane sun fito kwansu da kwarkwatarsu suna murna da godiya, suna addu’ar Allah ya saka wa Hon. Munira, bisa wannan aiki na alheri da ta kawo.

Mai magana da yawun Hon. Munira, Ibrahim Munir, wanda shi ne S.A Media and Publicity ga Shugabar Marasa Rinji, ya bayyana cewa wannan aikin wani bangare ne na jajircewar Zinariyar Saminaka wajen ciyar da jama’a gaba.

Copyright © 2024 kaduna Reports.