Her Excellency, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, ta kaddamar da sabon reshen Foresight Premier Hospital a garin Kaduna, tare da jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu wajen inganta kiwon lafiya a jihar.
A jawabin da ta gabatar a wajen taron, Dr. Hadiza ta bayyana cewa, “ba gwamnati kadai za ta iya daukar nauyin bayar da ingantaccen kiwon lafiya ba. Dole ne a samu cikakken hadin gwiwa da kamfanonin masu zaman kansu domin cimma nasara.”
Ta kara da cewa fadada ayyukan asibitin zuwa Kaduna zai taimaka matuka wajen ceto rayuka da kuma kara karfin tsarin kiwon lafiya a jihar.
Ta bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna tana ba da fifiko sosai ga fannin kiwon lafiya, inda take ware akalla kashi 15 cikin 100 na kasafin kudinta ga kiwon lafiya, kamar yadda kungiyoyin kasa da kasa suka ba da shawara.
Kalubale da Shawarwari
A nasa jawabin, shugaban taron, Farfesa Idris Muhammad Bugaje, wanda shi ne Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Fasaha ta Kasa (NBTE), ya bayyana damuwa kan manyan matsalolin da ke hana samun ingantaccen kiwon lafiya a Najeriya.
Ya lissafa wasu daga cikin matsalolin da suka hada da: Karancin ma’aikatan lafiya, Dangantaka mara kyau tsakanin likitoci da marasa lafiya, Karancin kayan aiki da gine-gine da kuma Rashin tsayayyen tsarin kudade.
Farfesa Bugaje ya bukaci gwamnati da ta samar da hanyoyin dorewar kudade, karin ma’aikata masu inganci, da kuma hada magungunan gargajiya da na zamani. Haka kuma, ya bukaci a fadada tsarin inshorar lafiya.
Burin Foresight Premier Hospital
Shugaban gudanarwa na Foresight Premier Hospital, Dr. Shamsuddeen A. Aliyu, ya bayyana cewa burin asibitin shi ne samar da kiwon lafiya mai inganci, wanda kowa zai iya samu cikin sauki .
“Ayyukanmu sun ta’allaka ne kan saukaka wa ‘yan Najeriya samun lafiyar jiki da na zuciya, tare da zama jagora wajen bayar da kulawa ta musamman a Najeriya,” in ji Dr. Aliyu.
Asibitin Foresight Premier na daga cikin sabbin cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu da ke da burin kawo sauyi mai dorewa a tsarin kiwon lafiya a Najeriya.