A wani yunƙuri na nuna ƙarfin tattalin arzikin Kaduna a idon duniya, Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Hadiza Balarabe, ta jagoranci wani muhimmin taro na kwamitin da aka kafa don shiryawa halartar taron cinikayya na Intra-African Trade Fair (IATF2025).
Taron IATF2025 wanda zai gudana daga ranar 4 zuwa 10 ga Satumba, yana sa ran karɓar baƙi fiye da 35,000 daga ƙasashe sama da 140.
An shirya wannan babban taro ne tare da haɗin gwiwar bankin Afreximbank da Hukumar Tarayyar Afirka (AU), domin bunƙasa cinikayya da zuba jari a nahiyar.
A cewar Mataimakin Gwamnan, wannan shiri yana da matuƙar muhimmanci don tabbatar da cewa Jihar Kaduna ta nuna kanta a matsayin mafakar masu zuba jari da ‘yan kasuwa.
Tana mai cewa jihar na da arzikin noma, yawan matasa masu hazaka, da kuma kyakkyawan yanayi na zuba jari.
Ana sa ran Kaduna za ta gabatar da cikakken labari mai ƙarfafa gwiwa ga masu zuba jari da abokan ciniki, domin jawo hannun jari daga ƙasashen waje, ƙirƙirar damammakin tattalin arziki, da buɗe kasuwanni don kayayyakin cikin gida.
Wannan shiri ya yi daidai da manufofin ci gaban tattalin arziki na Gwamna Uba Sani, wanda ke da nufin canza rayuwar al’umma ta hanyar inganta masana’antu, noma, da kasuwanci a jihar.