Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Illimi

Majalisar Wakilai Na 10 Ta Dage: Kakakin Majalisa Ya Sami Digirin Girmamawa Daga Jami’ar NOUN

Published

on

Kakakin Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya samu gagarumar girmamawa yayin bikin yaye daliban jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN) karo na 14, inda aka bashi digirin girmamawa na Doctor of Business Administration (DBA).

Rt. Hon. Abbas ya bayyana wannan lambar yabo a matsayin girmamawa tare da godiya, yana mai jaddada muhimmancin ilimi wajen sauya rayuwar al’umma da ƙasar gaba ɗaya.

“Ba kawai a matsayin Kakakin Majalisa ba, har ma a matsayin wanda ke da kishin ilimi, na fahimci cewa lokaci ya yi da za a yi garambawul mai zurfi ga fannin ilimi a Najeriya,” in ji shi.

Ƙarfafa Matasa da Sauya Fannin Ilimi

Kakakin ya ce matasa sune ginshikin cigaban kowace ƙasa, kuma Majalisar Wakilai ta 10 na aiki kafada da kafada domin: Inganta ababen more rayuwa a makarantu, Ƙara kuɗaɗen tallafi da bincike, Fadada damar samun ilimi ta hanyar lamunin ɗalibai, Samar da sababbin cibiyoyin koyon sana’o’i da fasaha.

“Muna da burin kafa tsarin ilimi da zai samar da cancanta, ƙwarewa, da damammaki na ainihi ga matasanmu,” in ji Kakakin.

Girmamawa Ga Jagororin Ilimi

A yayin bikin, Kakakin ya kuma taya Dr. Akinwumi Adesina, shugaban Bankin Cigaban Afirka (AfDB), murna bisa samun digirin girmamawa na Doctor of Humane Letters. Ya kuma miƙa godiya ga Mai Martaba Oba Ewuare II, wanda shi ne Chancellor na jami’ar, da Farfesa Olufemi Peters, Shugaban Jami’a, da kuma dukkanin al’ummar NOUN.

Rt. Hon. Abbas ya jaddada cewa ba zai yi ƙasa a guiwa ba wajen aiwatar da manufofin da suka dogara da bincike da ilimi, domin ciyar da Najeriya gaba.

“Lokaci ne da za mu ɗinke gibin da ke tsakanin ilimi da damar rayuwa,” in ji shi.

Copyright © 2024 kaduna Reports.