Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Majalisar Kaduna ta Amince da Dokar Kafa Hukumar Kula da Makarantun Sakandare

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudurin doka da zai kafa Hukumar Kula da Makarantun Sakandare a jihar.

An amince da kudurin ne bayan karatu na uku da tattaunawa tsakanin ‘yan majalisar.

Shugaban kwamitin ilimi na majalisar, Hon. Mahmud Lawal, wanda ke wakiltar mazabar Zaria City, ya ce dokar za ta taimaka wajen tsara ayyukan makarantun sakandare da kuma hada ayyukan Hukumar Kula da Malamai (Teachers Service Board) cikin tsari guda.

Ya kara da cewa, kafa wannan sabuwar hukuma zai bai wa Jihar Kaduna damar samun karin tallafi daga gwamnatin tarayya domin bunkasa ilimin sakandare.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.