Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

MACBAN Kaduna: Kwamishinan Tsaro Ya Bukaci Zaman Lafiya

Published

on

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Sir James Atung Kanyip (PhD), ya bukaci shugabannin Fulani da su kasance jakadun zaman lafiya da fahimta a tsakanin al’umma.

Ya bayyana haka ne yayin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN), reshen jihar Kaduna, wanda ya gudana a babban birnin jihar.

A cikin sakon taya murna da ya gabatar, Kanyip ya yi kira ga sabon shugaban MACBAN na jihar Kaduna, Abdulhamid Musa Alabarka, da sauran mambobin kwamitin zartarwa, da su kasance masu gina amana tsakanin Fulani da sauran al’umma.

“Lalle akwai bukatar mu canza yadda ake kallon Fulani a idon duniya. Dole ne mu kafa tarihi ta hanyar nuna halin kirki, zaman lafiya da kishin kasa,” in ji Kanyip.

Kwamishinan ya kuma jaddada cewa gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani tana jajirce wajen ganin an samu daidaito da kwanciyar hankali a tsakanin manoma da makiyaya.

Ya ce irin wannan taro yana da muhimmanci wajen karfafa zumunci da hadin kai tsakanin shugabanni da mabiyansu, musamman a lokaci da ake fuskantar kalubale na tsaro.

Sabon shugaban MACBAN, Abdulhamid Musa Alabarka, ya gode wa Kwamishina Kanyip bisa halartar bikin, tare da sha alwashin cewa sabbin shugabannin za su yi aiki kafada da kafada da hukumomi don inganta zaman lafiya da cigaban kiwo.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.