Kwamishinan lafiya ta jihar Kaduna yayin gudanar da taro.
A yau, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna ta gudanar da taron gudanar da ayyuka na yau da kullum, wanda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma K. Ahmed, ta jagoranta.
A cikin jawabinta na maraba, Kwamishiniyar ta jaddada muhimmancin jajircewa da kirkire-kirkire a tsakanin dukkan sassan ma’aikatar, domin tabbatar da cewa an aiwatar da ayyuka bisa inganci da nagarta.
Taron na nuni da kudirin Ma’aikatar Lafiya na ci gaba da inganta yadda ake gudanar da ayyuka da kuma tabbatar da ingantacciyar hidimar kiwon lafiya ga al’ummar Jihar Kaduna.
Manufofin taron sun haɗa da: Nazarin ayyukan sassa daban-daban, tsara dabarun aiki na gaba, karfafa haɗin gwiwa tsakaninma’aikatar da hukumomi da kuma samar da hanyoyin magance ƙalubale
A ƙarshen taron, ana sa ran za a samar da tsare-tsaren da za a aiwatar domin ci gaba da ƙarfafa ayyukan ma’aikatar da inganta kiwon lafiyar al’umma a Jihar Kaduna.