Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gida na Jihar Kaduna, Sir James A. Kanyip KSM; PhD, ya karɓi bakuncin Shugaban Kungiyar Masu Adaidaita Sahu ta Jihar Kaduna, Alhaji Garba Rabiu Giwa.
Ziyarar wanda ya gudana a gidan Sir Kashim Ibrahim House dake birnin jihar Kaduna, a ranar litini.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan magance manyan ƙalubalen tsaro da suka shafi ayyukan Adaidaita Sahu (Keke Napep) da Babura (Okada) a fadin jihar. Hakazalika, an tattauna hanyoyin da za a bi don ƙara tabbatar da tsaro da inganta ayyukan sufurin jama’a a jihar.
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na ci gaba da aiki tare da kungiyoyi da hukumomi masu ruwa da tsaki don tabbatar da kare lafiyar al’umma da samar da ingantacciyar doka da oda a harkar sufuri.
Taron ya kasance wani muhimmin mataki na ƙoƙarin gwamnatin Jihar Kaduna na magance matsalolin tsaro da inganta jin daɗin al’ummar jihar.