Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Gida na Jihar Kaduna, Sir James A. Kanyip, KSM; PhD, ya jagoranci bikin mika ragamar ofishin Kwamandan Hukumar Tsaro ta Vigilante ta Jihar Kaduna (KADVS) da aka gudanar a ofishinsa da ke Sir Kashim Ibrahim House, Kaduna.
Tsohon Kwamanda, Brigadier Janar (Rtd) Umar Muhammad Ibrahim, wanda ya yi aikin tsawon shekara uku da wata takwas, ya bayyana godiyarsa ga ma’aikatan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida bisa hadin kai da goyon baya da suka nuna masa a lokacin aikinsa.
A jawabinsa, Kwamishina Kanyip ya yabawa Brig. Janar (Rtd) Umar Ibrahim a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a tsarin tsaron Jihar Kaduna. Ya jinjinawa kwazon da ya nuna wajen inganta harkokin tsaro.
Kwamishinan ya shawarci sabon Kwamanda, Kwamishinan ‘Yan Sanda (Rtd) Ali D. Audu, da ya ci gaba daga inda wanda ya gada ya tsaya.
Ya bukace shi da ya gina KADVS mai tsari da ladabi, tare da karfafa haɗin kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin Jihar Kaduna.