Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Kwalejin Man Fetur Na Kaduna ya Kusan Fara Aiki – Minista

Published

on

Ministan harkokin man fetur mai kula da iskar gas, Ekperikpe Ekpo, ya ce an kusa kammala aikin gina Kwalejin Nazarin Man Fetur da Makamashi da ke Kaduna.

Ministan ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a cikin kwalejin ranar Juma’a.

Ya ce aikin ginin kwalejin ya kai kashi 90 cikin 100, kuma saura ‘yan kwanaki a gama shi.

Kwalejin dai na kan hanyar Kaduna-Zaria, kusa da kasuwar baje kolin ta Kaduna, kuma an fara aikin fiye da shekaru 15 da suka wuce.

“Mun zo da farko muna ganinsa a kashi 60, amma yanzu ya kai 90 cikin 100,” in ji ministan.

Ya yaba da kokarin hukumar PTDF karkashin jagorancin Ahmed Galadima Aminu, inda ya ce kwalejin na da dakin karatu na zamani da cibiyar taro ta kasa da kasa.

Ministan ya ce kwalejin za ta taimaka wajen horar da kwararru a fannin makamashi tare da rage yawan tura dalibai kasashen waje.

Ya ce ana sa ran fara karatu a kwalejin a shekarar 2025.

A nasa bangaren, Babban Sakataren PTDF, Ahmed Galadima Aminu, ya ce sun riga sun karɓi takara nema 531 daga dalibai.

Kwalejin na da gine-gine na karatu da masauki, wuraren ibada, da filin motsa jiki, a kan fili mai fadin hekta 86.

Ya ce ana da haɗin gwiwa da jami’o’in Birtaniya da kuma NNPC Academy domin horar da dalibai.

“Muna fatan kaddamar da kwalejin cikin ‘yan makonni masu zuwa,” in ji shi.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.