Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

Komishinan Tsaro Na Cikin Gida, Sir James Kanyip, Ya Halarci Taron Kasa Na Gina Zaman Lafiya a Abuja

Published

on

Kwamishinan Harkokin Tsaro na Cikin Gida da Al’amuran Gida na Jihar Kaduna, Sir James A. Kanyip, KSM; PhD, ya halarci taron kasa kan gina zaman lafiya da aka gudanar jiya a cibiyar sulhu da warware rikice-rikice ta kasa (IPCR), a garin Abuja.

Taron wanda Integrity and Compliance Management Consult ta shirya, ya tattara kwararru da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasa domin tattauna dabarun zaman lafiya mai ɗorewa.

Dr. Paul Andrew Gwaza, wanda shi ne mai magana da yawun taron, ya taka muhimmiyar rawa wajen bayyana manufofi da kuma jagorantar muhawara kan hanyoyin magance rikice-rikice da kafa zaman lafiya mai inganci.

Tattaunawar ta fi mayar da hankali ne kan fahimtar tushen rikice-rikice da kuma amfani da hanyoyi masu ma’ana da haɗin kai wajen gina zaman lafiya a al’umma.

Sir James Kanyip ya bayyana muhimmancin irin waɗannan taruka wajen inganta tsaro da haɗin kai a Najeriya, tare da jaddada cewa gwamnatin Jihar Kaduna za ta ci gaba da mara baya ga ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

Copyright © 2024 kaduna Reports.