Jakadan kasar Italiya a Najeriya, H.E. Lacopo Foti, ya kai ziyara ta farko a jihar Kaduna domin tattaunawa kan yadda za a karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Italiya da jihar Kaduna.
An tarbe shi ne a fadar gwamnatin jihar Kaduna a gidan Sir Kashim Ibrahim, inda mataimakiyar gwamnan jihar, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta karbe shi a madadin gwamnatin jihar.
Jakadan ya bayyana cewa gwamnatin Italiya na da sha’awar ganin kamfanonin Italiya sun fara zuba jari a jihar Kaduna, musamman a bangarorin injiniya, masana’antu, noma, ilimi da horar da matasa. Ya kuma bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta gabatar da cikakken tsarin jari wanda za a iya tallafawa ta ofishin jakadancin Italiya.
A nata bangaren, Dr. Hadiza Balarabe ta jaddada cewa jihar Kaduna na da manyan damammaki a fannonin noman zamani (musamman masara, tumatur da citta), albarkatun kasa, yawon bude ido, makamashi, fasahar zamani da ci gaban matasa.
Ta kuma umurci hukumar tallafawa zuba jari ta jihar Kaduna (KADIPA) da ta gaggauta hada da mika cikakken tsarin zuba jari zuwa ofishin jakadancin Italiya.
Dukkan bangarorin biyu sun nuna kwarin gwiwar cewa za a kafa manyan hadin gwiwa da za su amfani al’ummar Kaduna da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.