Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Ko Kun San?

Kasafin Kuɗi Kananan Hukumomin 23 na Jihar Kaduna na Shekarar 2025 Ya Kai Naira Biliyan 123.3

Published

on

An amince da kasafin kudin kananan hukumomin Jihar Kadun na shekarar 2025 wanda aka sanya wa taken “Ci gaba da Sauya Yankunan Karkara Domin Ingantaccen Cigaba” da kuma kudin da aka ware ya kai Naira biliyan 123.3.

Jimillar kasafin kuɗi na kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna da aka amince da su a shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 123.3, inda kudin da aka gabatar a farko ya kasance Naira biliyan 115.8. Wannan yana nufin an samu karuwar kaso 6% wanda ya kai Naira biliyan 7.5.

Idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda aka amince da kasafin kuɗi na Naira biliyan 107.2, an samu karuwar kaso 15% a kasafin kuɗi na 2025.

Dangane da rarraba kasafin kuɗi bisa ga mazabu uku na Sanatocin Jihar Kaduna, Kaduna South zai karɓi Naira biliyan 37.9, Kaduna Central Naira biliyan 41.0, yayin da Kaduna North zai samu Naira biliyan 44.3.

Jimillar kuɗin da za a samu daga haraji da sauran kudaden shiga na yau da kullum ya kai Naira biliyan 120.6 wanda ke wakiltar kaso 97.8%, yayin da kudaden da za a samu daga tallafin manyan ayyuka suka kai Naira biliyan 2.6, wanda ya wakilci kaso 2.2%.

Dangane da yadda za a kashe kuɗin, an ware Naira biliyan 55.3 don ayyukan raya kasa, yayin da za a kashe Naira biliyan 46.1 kan albashin ma’aikata, sai kuma Naira biliyan 21.8 don kudin gudanarwa wanda ke cikin ɓangaren kashe kudaden yau da kullum.

Copyright © 2024 kaduna Reports.