Karamar Hukumar Kachia da ke Jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta kashe Naira miliyan 205 don siyan motoci ga Shugaban Karamar Hukumar da Mataimakinsa a kasafin kudin shekarar 2025. Wannan na daga cikin kasafin kudin kananan hukumomin Jihar Kaduna na shekarar 2025 mai taken “Ci gaba da Sauya Yankunan Karkara Domin Ingantaccen Ci Gaba.”
A cewar bayanan kasafin kudin, an ware kudaden ne don sayen motoci ga shugabannin karamar hukumar domin sauƙaƙa gudanar da ayyukansu na yau da kullum. Bayan haka, kasafin ya nuna cewa an ware Naira miliyan 365 don ayukan cigaban more rayuwa, wanda shine mafi girman kaso a kasafin kudin raya kasa na karamar hukumar Kachia.
Bayanai Kan Kasafin Kudaden Sayen Motoci:
LG Code: 31830900
Fund’l. Code: 70451
Programme Code: 131001
Fund Code: 03101
Economic Code: 23010105
Kudin: Naira miliyan 205
Abin da za a yi: Siyan motoci ga Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa
Idan aka kwatanta da kasafin shekarar 2024, wanda aka ware Naira miliyan 20 don siyan motoci ga shugabannin karamar hukumar, sabon kasafin na 2025 ya nuna ƙaruwa kudi da kashi 925%.
Shin Kasafin Kudaden Zai Zama Gaskiya?
A matsayinsa na tsarin kasafin kudi, ba wai dukkan abubuwan da aka lissafa za a aiwatar da su kai tsaye ba. A cewar dokokin gudanar da kasafin kudi, sai idan gwamnati ta samu kudaden da ake bukata, sannan za a aiwatar da tanadin da ke cikin kasafin.