A ci gaba da kokarin Gwamna Uba Sani na bunkasa ingancin ilimin firamare a Jihar Kaduna, Shugaban Karamar Hukumar Kaduna North, Hon. Bashir Isah (The Lion), ta hannun Shugaban Ma’aikata, Hon. Muhammad Gambo ya wakilci shi wajen sa ido kan rabon kayan koyarwa ga dukkan makarantu na firamare a a karamar hukumar.
An gudanar da wannan aikin karkashin kulawar Sakatariyar Ilimi ta Karamar Hukumar, Hajiya Amina Sani (One Minute).
Kayan koyarwar da aka rabawa malamai sun hada da: Marker, Whiteboard, Takardu da sauran kayan koyarwa .
Hon. Bashir Isah (The Lion) ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin manufar gwamnatin Kaduna na tabbatar da cewa malamai suna da duk kayan aikin da suka dace domin bunkasa inganci da inganta kwarewar dalibai.
Hajiya Amina Sani (One Minute) ta kara da cewa za su ci gaba da lura da amfani da kayan domin tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata a ajin karatu.