A shekarar 2025 a nasa rai karamar hukumar igabi ta jahar Kaduna za ta kashe kimani naira miliyan 140 gun sanyan solar Kan hanya a fadin karamar hukumar.
Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna ta ware kimanin Naira miliyan 140 domin saka hasken solar a hanyoyin yankin a cikin kasafin kudinta na shekarar 2025. Wannan na daga cikin shirin karamar hukumar na inganta wutar solar a hanyoyin karamar hukumar.
Shirin na daga cikin kasafin kudin kananan hukumomi na 2025 mai taken “Ci gaba da Sauya Yankunan Karkara Domin Ingantaccen Ci Gaba.” A cewar bayanan kasafin kudin, an ware kudaden ne domin tabbatar da cewa hanyoyi a fadin karamar hukumar sun sami haske.
Tsarin Kudade Solar Da Karamar Hukumar Igabi Zata Kashe a Shekarar 2025
A cikin bayanan kasafin, an bayyana cewa kudaden sun kasance a karkashin wadannan lambobin shirin:
LG Code: 31820500
Fund’l. Code: 70436
Programme Code: 201001
Fund Code: 03101
Economic Code: 23020103
Wadannan kudade za a yi amfani da su wajen saka hasken solar a hanyoyi daban-daban na karamar hukumar Igabi.
An Samu Karin Kaso 536.36% daga Kasafin 2024
A cikin kasafin shekarar 2024, karamar hukumar Igabi, ta bayana kashe Naira miliyan 22 wajen sanya solar a hanyoyinta. Sabon kasafin na 2025 ya nuna karin kashi 536.36% idan aka kwatanta da na bara. Wannan karin na nuna cewa an kara himma wajen habaka wutar lantarki da inganta hanyoyi a karamar hukumar Igabi.