Shugaban karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, Hon. Muhuyideen A. Umar, ya jagoranci taron tsaro tare da jami’an tsaro da shugabannin al’umma domin duba halin tsaro a yankin.
A cikin matakan da aka dauka bayan taron, an:
Haramta noma a gefen hanya, musamman a hanyar Jere zuwa Kurmin Jibrin, saboda yana hana ruwa bi ta magudanan ruwa.
Haramta shuke-shuke masu tsawo a cikin gari, saboda ana amfani da su a matsayin maboyar masu aikata laifi.
Bukaci manoma su kare hanyoyin kiwo (labi) don saukaka zirga-zirgar makiyaya.
Gargadi jama’a su kula da layukan wutar lantarki, duba da aikin dawo da hasken lantarki da ake yi a wasu yankuna.
Shugaban ya ce hadin kan al’umma da hukumomi na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a Kagarko.