Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Yajin Aikin ASUU-KASU 2025 Karo Na Biyu

Labarai

KADUNA: Taron JAAC Na Watan Maris 2025 Ya Bayyana Kasafin N11.75BN Ga Kananan Hukumomi 23

Published

on

Jihar Kaduna ta gudanar da taron kwamitin raba kudaden asusun hadin gwiwa (JAAC) na watan Maris 2025.

Taron wanda ya gudana a ranar Laraba 9 ga Afrilu, a Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu.

Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe itace ta jagoranci taron, tare da samu halartar Kwamishinan Kananan Hukumomi, Hon. Sadiq Maman Lagos, manyan jami’an ma’aikatar, shugabannin kananan hukumomi 23 da kuma wakilan hukumomin da ke cikin JAAC.

A cewar bayanan da aka gabatar, jimillar kudaden da aka samu daga Asusun Tarayya ga kananan hukumomi 23 a watan Maris ya kai Naira biliyan 11.75, inda harajin cikin gida (IGR) da suka tara ya kai Naira miliyan 32.13 kamar yadda hukumar KADIRS ta bayyana.

Takaitaccen Rarraba Kudaden:

Rabon Kudaden Doka (Statutory Allocation): N4,991,461,173.22

Rabon Harajin VAT: N6,208,941,609.60

Rabon Haranji Daga Electronic Transfer (EMT): N373,385,075.85

Rabon Karin Kudi (Augmentation): N176,253,870.38

Kwamishinan Kananan Hukumomi ya jaddada cewa wannan rabon kudade zai tallafa wajen aiwatar da ayyukan cigaba a matakin ƙananan hukumomi, musamman samar da ayyuka da tallafi ga al’umma.

Mataimakiyar Gwamna ta yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da su tabbatar da amfani da kudaden cikin gaskiya da inganci domin jin dadin jama’a.

Copyright © 2024 kaduna Reports.