Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaddamar da sabon kwamitin sanya ido da aka faɗaɗa kan Basic Health Care Provision Fund (BHCPF) domin inganta amfani da tallafin lafiyar jama’a.
An kaddamar da kwamitin ne a dakin taron Ma’aikatar Lafiya karkashin jagorancin Kwamishinar Lafiya, Hajiya Umma K. Ahmed. Ta bayyana cewa shirin BHCPF na da matuƙar muhimmanci wajen kula da lafiyar alumma, musamman mata da yara.
Hajiya Umma ta jaddada cewa faɗaɗa kwamitin na nuna irin ƙudurinsa Gwamna Uba Sani na tabbatar da gaskiya, adalci da haɗin kai a harkar lafiya. Ta bukaci mambobin kwamitin da su haɗa kai, su tabbatar da ingantaccen aiki da tsabtace tsarin kashe kudaden lafiya.
Kwamitin ya haɗa wakilai daga gwamnati, ƙungiyoyin raya al’umma, na addini, da kuma sarakunan gargajiya. Za su duba ayyukan cibiyoyin lafiya, su tabbatar da komai yana tafiya daidai.
Wannan mataki ya ƙara tabbatar da burin gwamnatin Kaduna na samar da ingantacciyar kulawa ta lafiya ga kowane ɗan jiha, ba tare da wariya ba.