Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana shirye-shiryen karɓar zuba jari na dala miliyan 300 a fannin ma’adinai a jihar.
Gwamna Uba Sani ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da ya yi da Colin Ikin, Manajan Darakta na kamfanin Atlantic Mining Techniques Ltd.
Gwamnan ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan haɓaka sashen ma’adinai na jihar, da kuma kafa katafaren kamfani da zai sarrafa ma’adinai a Kaduna.
Ya ce wannan wani bangare ne na ci gaba da aka samu bayan kafa masana’antar sarrafa Lithium a jihar – daya daga cikin na farko a Najeriya.
Gwamna Uba Sani ya ce Kaduna na da manyan albarkatu na ma’adinai, kuma tana da ƙa’idodi da rangwame da suka dace don jawo masu saka jari daga ciki da wajen Najeriya.
Ya ce gwamnati za ta ci gaba da kare duk wani jari da ke shigowa jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya da sauƙin gudanar da kasuwanci.