…Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki Ta Ba da Wa’adin Kwana Bakwai
An shiga wani sabon rikici a bangaren wutar lantarki a Kaduna, yayin da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) ta ba Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) wa’adin kwana bakwai domin komawa teburin tattaunawa.
Takaddamar ta fara ne bayan kamfanin ya aika wa wasu ma’aikatansa da takardun sallama da ke nuna cewa “ba a sake bukatarsu.” NUEE ta ce wannan mataki ya saba wa yarjejeniyoyin da aka cimma a baya.
Jami’in NUEE na Arewa maso Yamma, Ayuba Pukat, ya bayyana cewa shugabannin Kaduna Electric sun yi watsi da tattaunawar da aka fara, tare da ci gaba da sallamar ma’aikata ba tare da karin bayani ba.
Kaduna Ta Fuskanci Duhu na Kwanaki Biyar
Tun a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki na sai baba-ta-gani saboda shirin sallamar sama da ma’aikata 900. Wannan yajin aiki ya haifar da matsalar wuta, inda Kaduna ta fada cikin duhu na tsawon kwanaki biyar.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya shiga tsakani, lamarin da ya kai ga dakatar da yajin aikin tare da alkawarin cewa za a ci gaba da tattaunawa. Sai dai bayan kimanin wasu makonni, kungiyar NUEE ta ce kamfanin bai cika alkawarin ba, hakan yasa suka sake gindaya sabon wa’adi.
Shin Za a Sake Yajin Aiki ?
Idan har kamfanin bai saurari bukatun ma’aikatan ba cikin kwanaki bakwai masu zuwa, akwai yiwuwar sake shiga yajin aiki, wanda ka iya haddasa sabon matsalar wuta a Kaduna da kewaye.
Masu amfani da wutar lantarki a jihar na fargabar sake fuskantar matsala, inda wasu ke kira ga gwamnati da ta shigo tsakani domin gujewa wani sabon duhu da ka iya hana ayyukan yau da kullum ci gaba.
Ana sa ran bangarorin biyu za su koma teburin tattaunawa domin gujewa sake fadawa matsalar da za ta shafi dubban al’umma.