Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

KADIRS Ta Karyata Zargin Rufe Hanyar Kaduna-Abuja Saboda Karɓar Haraji

Published

on

Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta nesanta kanta daga rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta da wani gidan rediyo ya wallafa, inda aka ce rufewar hanyar Kaduna zuwa Abuja da aka gani ranar Asabar, 3 ga Mayu, ta faru ne sakamakon karbar haraji da jami’an gwamnati ke yi.

A cikin wata takardar manema labarai da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Zakari Jamilu Muhammad, ya fitar a ranar Litinin, KADIRS ta bayyana cewa ba ta da hannu ko alaka da rufe hanyar da aka yi.

Ta ce babu wani jami’inta ko wakilinta da ya halarci ko ya jagoranci wannan abu da aka aikata.

A cewar hukumar, bisa tanadin sashe na 104, karamin sashe na biyu cikin baka na dokar haraji ta Jihar Kaduna ta 2020, babu wani mutum ko hukuma da ke da ikon rufe hanya domin karbar haraji ko tara a fadin jihar.

“Wannan rufewar hanya da ake magana a kai, ba jami’anmu suka yi ba.
Babu kuma wani da muka ba izini ya wakilce mu wajen karbar kudi ko tara a hanya,” in ji sanarwar.

KADIRS ta kuma bukaci kafar yada labaran da ta wallafa rahoton da ba ta tantance gaskiyarsa ba da ta gaggauta janyewa tare da fitar da gyara.

Haka kuma, hukumar ta ja hankalin sauran kafafen watsa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai da suka shafi haraji kafin su wallafa su, ta hanyar tuntubar hukumar da ta dace.

A wani mataki na gyara da inganta tsarin karbar haraji a Jihar Kaduna, KADIRS ta gudanar da taron haɗin guiwa da manyan shugabannin kungiyoyin direbobi na ƙasa (NURTW, RTEAN, da NARTO) a ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025, a shelkwatar hukumar da ke Kaduna.

An gudanar da taron ne a ƙarƙashin jagorancin Daraktan Gudanarwa kan Haraji, Dr. Muhamud Lawal, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar Haraji na Jihar Kaduna.

A taron, an cimma matsaya kan kafa kwamitin hadaka (JTB) da zai duba yadda ake karbar haraji, tabbatar da tsarin karba cikin gaskiya da adalci, da kuma amfani da mambobin kungiyoyin don gano masu karbar haraji ba bisa ƙa’ida ba a titunan jihar.

Dukkanin bangarorin sun bayyana niyyar yin aiki tare da KADIRS domin magance matsalar haraji maras tushe da hana rufe hanyoyi da sunan tara kudi.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.