Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Comrade Jerry Adams, ta karɓi tawagar shugabannin Kungiyar Direbobin Babura ta Najeriya (MOUN), reshen Jihar Kaduna, a wata ziyarar ban girma da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Kaduna.
Bayanin taron na kunshe ne a wata sanarwa da Zakari Jamilu Muhammad Shugaban Sashen Hulda da Jama’a, KADIRS ya fitar a ranar 29 ga watan Afirulu, 2025.
Taron ya gudana ne tare da halartar Babban Daraktan Tsare-tsare da Bin Doka, Alhaji Ali Garba Gora, da wasu manyan jami’an hukumar. A jawabinsa, Shugaban KADIRS ya yabawa kungiyar bisa irin goyon bayan da suke baiwa gwamnati duk da haramcin zirga-zirgar babura da ke ci gaba da aiki a jihar.
Comrade Jerry Adams ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayar da umarnin kaddamar da tattaunawa tsakanin hukumomin KASTRA, MISHA, KASTLEA da KADIRS domin tsara hanyoyin da za su kai ga sassauta haramcin, tare da la’akari da batutuwan tsaro da samar da kudaden shiga ga jihar.
Shugaban tawagar MOUN ya nuna jin daɗin sa ga gwamnatin jihar bisa manufofin da ke sauƙaƙa wa al’umma, tare da tabbatar da cewa kungiyar za ta ci gaba da bin doka da ƙa’idojin aiki. Haka kuma, ya bayyana cewa kungiyar za ta hada gwiwa da KADIRS wajen yaki da masu tarar haraji ba bisa ka’ida ba da kuma dakile ayyukan ‘yan daba da ke damun ‘yan kasuwa da direbobi.
Taron ya samu halartar Hajiya Asmau Inuwa Mora (Daraktar Harajin Shiga Kai Tsaye), Mr. Ishaku Mazan Gona (Daraktan Tsare-tsaren Haraji), Alhaji Ya’u Kauru (Shugaban Sashen Harkokin Sufuri), da sauran shugabannin sassa daga hukumar KADIRS.