Jihar Kaduna ta kafa tarihi a fannin bunkasa noma a Najeriya, inda ta zama jiha ta farko da ta kaddamar da Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) a kasar.
Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB), Dr. Akinwumi Adesina, ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Uba Sani a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim ranar Talata.
A cewar Dr. Adesina, “Kaduna jiha ce da ke da hangen nesa wajen tabbatar da wadatar abinci, bunkasar tattalin arziki da ci gaban al’umma. Wannan aikin ya nuna jajircewa da kwazon shugabanci.”
Ya jinjinawa Gwamna Uba Sani bisa karin kasafin kudin noma daga Naira biliyan 1.4 a 2023 zuwa Naira biliyan 74 a 2025, yana mai cewa hakan na nuna cikakken goyon baya da zuba jari daga gwamnati.
“Ba wai kawai ku saka kudi a inda bakin ku yake ba ne – ku saka kudi a inda zuciyar ku da jikin ku suke,” in ji Dr. Adesina, lamarin da ya jawo tafi daga mahalarta taron.
Dr. Adesina ya kara da cewa AfDB za ta ci gaba da tallafawa Kaduna a bangaren shirin ciyar da dalibai a makarantu, da inganta kiwon lafiya, inshorar lafiya, ruwan sha, da saukaka tsarin dijital a jihar.
Kaduna Ta Zama Jagora
Shugaban AfDB ya bayyana Kaduna a matsayin jiha mai jagoranci da kishin kasa, yana mai cewa: “Ku ne na farko da kuka kaddamar da SAPZ a Najeriya. Wannan rana ce mai tarihi a gare mu duka.”
Ya kuma jinjinawa karimcin jihar da cewa: “Ba kawai mun samu karimci ba a Kaduna — hatta mataimakiyar gwamna ku likita ce, don haka mun samu ‘maternity’ ma!”
Gwamna Uba Sani Ya Yabawa Adesina
Gwamna Uba Sani ya bayyana Dr. Akinwumi Adesina a matsayin “albarka ga Najeriya, Afirka da duniya baki daya.”
Ya kuma jaddada cewa lokacin da Dr. Adesina ke matsayin Ministan Noma a Najeriya, ya kirkiro manhajar E-wallet da ta taimakawa fiye da manoma kanana miliyan 15, yawancinsu daga Arewacin Najeriya.
“Wannan tsari zai iya rage matsalar rashin shigar kudi, da taimakawa wajen yaki da rashin tsaro da ke hana ci gaban noma a Arewacin Najeriya,” in ji gwamnan.
Ya kuma bayyana cewa a Kaduna, noma na da kashi 42 cikin 100 na GDP da kuma kashi 60 cikin 100 na aikin yi, yana mai cewa saboda haka ne gwamnati ta zuba jari mai yawa don karfafa fannin.