Connect with us
Blinking Dot and Text
Ku Saurare Mu Kaitsaye
Kai Tsaye:
Babu sabbin labarai a yanzu.

Labarai

Jihar Kaduna Na Daga Cikin Jerin Jahohin Dake Zaman Lafiya – Gwamna Uba Sani

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da suka fi samun zaman lafiya a Najeriya a halin yanzu. Wannan na zuwa ne bayan shekara biyu ba tare da wani rikicin addini ko na kabilanci ba a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar Sir Kashim Ibrahim, yayin da yake mika motocin aiki guda 23 ga shugabannin gargajiya a fadin jihar a ranar Lahadi.

Ya ce: “Shugabannin gargajiya suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya. A kullum suna hada kai da jami’an tsaro, suna bayar da bayanan sirri, tare da kasancewa kusa da al’umma a kowane mataki.”

Gwamnan ya kara da cewa, wannan hadin gwiwa da shugabannin gargajiya na daga cikin manyan dalilan da yasa dabarun non-kinetic na gwamnati wajen yaki da rashin tsaro ke aiki yadda ya kamata.

KA/KI NA DA LABARI ?

Muna maraba da labarai daga gare ku. Idan ka/ki na da wani abu da ya dace da wallafa, a turo mana ta imel:

kadunareports@gmail.com

Copyright © 2024 kaduna Reports.