Gwamnatin Jihar Kaduna ta raba jimillar Naira biliyan 11.67 daga Asusun Tarayya ga kananan hukumomi 23 domin watan Afrilu, kamar yadda aka bayyana a taron Kwamitin Raba Kudaden Shiga (JAAC) karo na hudu.
Mataimakiyar Gwamna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ce ta jagoranci taron wanda aka gudanar a Ma’aikatar Harkokin Kananan Hukumomi ranar Alhamis.
Kwamishinan Harkokin Kananan Hukumomi, Hon. Sadiq Maman Lagos, ya gabatar da rahoton jimilar kididigan kudin a gun taron.
Naira miliyan 270.82 – Daga Harajin Canjin Kuɗi ta Intanet (Electronic Transfer Levy).
Naira miliyan 182.65 – Karin Kudi (Augmentation).
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, cikin watan idan aka duba, kananan hukumomin jihar sun samar da Naira miliyan 18.83 a matsayin kudin shiga na cikin gida (IGR).
Taron ya samu halartar shugabannin kananan hukumomi 23, da kuma shuwagabannin hukumomi da sassan gwamnati da ke da ruwa da tsaki a JAAC.