Iyalan Lance Corporal Auwal Shehu, wani soja da ya rasa ransa a wani hari da Boko Haram suka kai a garin Marte, Jihar Borno, sun samu tallafi daga dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna North, Hon. Bello El-Rufai.
A cewar Saifullahi Abdussamad, daya daga cikin wanda suka jagoranci isar da kayan, tallafin ya hada da buhun shinkafa, taliya da sauran kayan abinci da kudade har Naira dubu 300.
An bayar da Naira dubu 200 ga mahaifin marigayin, yayin da mahaifiyarsa ta samu Naira dubu 100.
Hon. Ahmad Makama da Shamsu S. Adam sun kasance cikin tawagar da ta mika gudummawar a madadin dan majalisar.
An bayyana cewa wannan tallafi ya zo ne biyo bayan jawabin da Hon. Bello El-Rufai ya yi na jajantawa da nuna alhini kan mutuwar sojan a bakin aiki.